✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojojin Faransa sun fara ficewa daga Nijar

Sojojin Faransa sun fara ficewa daga Nijar, inda sabuwar gwamnatin sojin kasar ta ce ba ta bukatarsu

A yau Talata sojojin Faransa suka fara ficewa daga Jamhuriyar Nijar, bayan matsin lamba daga gwamnatin sojin Janar Tchiani da ta ce ba ta bukatar su.

A safiyar nan kakakin shugaban ma’aikatan Faransa ya tababtar cewa “rukunin farko na dakarun“ sun fice daga Nijar.

A ranar Litinin gwamnatin sojin Nijar ta sanar cewa sojojin na Faransa mai dakaru 1,400 a Nijar saz su fara barkin kasar da rakiyar sojojin Nijar.

A watan Yuni sojojin Nijar suka hambarar da gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum da ke dasawa da Faransa, inda bayan nan suka bukacin sojojin Farsa da ke kasar su san inda dare ya yi musu.

Faransa ta kafa sansanonin sojinta a Nijar da kasashen Mali da Burkina Faso masu makwabtaka da Nijar ne domin taimaka musu yakar ’yan ta’adda.

Sai dai daga baya al’ummar kasashen na zargin turawan da rashin tsinana komai, hasali ma, suna zargin su da ba goyon bayan ’yan ta’addar da ba su damar cin karensu babu babbaka.

Bayan juyin mulkin da sojojin kasashen na Sahel suka yi, suka kori sojojin na Faransa, inda suka dawo Nijar, a zamanin Bazoum.

Bayan hambarar da shi kuma sojojin suka ce Faransa ta bar musu kasa suka kuma haramta wa jiragen ta shawagi a sararin samaniyar Nijar, lamarin da aka yi ta cacar baki a kai.

A watan da ya gabata ne Jakadan Faransa da jami’ansa suka fice daga Nijar, inda a lokacin ne aka sanar cewa a watan Oktoba sojojin za su biyo baya, inda zuwa karshen watan Disamba zamansu a Nijar zai zama tarihi.