✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Isra’ila sun rushe gidaden mutane 187,500 a Gaza a kwana 2 —MDD

Isra'ila ta kashe 'yan jaridar Falasdinawa uku a safiyar Talata bayan lalata gidaje 187,500 a Zirin Gaza inda ta hana safarar abinci tare da yanke…

Majalisar Dinkin Duniya ta ce haramun ne matakin da Isra’ila ta dauka na yi wa yankin Gaza kawanya.

Hakan na zuwa ne a yayin da ta bayyana cewa Falasdinawa 187,500 ne suka rasa muhallansu a yankin na Gaza daga lokacin da Isra’ila ta kaddamar da luguden wuta da jirage ranar Asabar zuwa yanzu.

Manzon MDD kan kare hakkin bil Adama, Volker Turk, ya ce dokar duniya ta haramta, “tare mutane a yanayin da rayuwar farar hula ke cikin hadari, ta hanyar hana su samun abinci da suran bukatun rayuwa.”

Volker Turk ya ce wajibi ne a mutunta dan Adam da rayuwarsa, inda ya yi kira ga bangarorin da ke yaki da juna su kai zuciya nesa.

Kungiyar mayakan Hamas na Falasdinawa da ta kai wa Isra’ila harin ba-zata a ranar Asabar tare da kashe yahudawa sama da 600 ta yi barazanar kashe mutum 150 da ta yi garkuwa da su, idan Isra’ila a ci gaba da kai hari barkatai kan yankin Gaza.

Hamas ta ya barazanar ce bayan a ranar Litinin Isra’ila ta katse hanyoyin kai abinci da ma wutar lantarki da ruwan sha, ta kuma hana shiga ko fita daga yankin Gaza.

Matakin na Isra’ila, wadda ta kai hare-hare sama da 500 a a Gaza, ya haifar da karin fargaba game da matsin rayuwar da al’ummar za su shiga a daidai lokacin da suke bukatar agaji.

“Dokar kasa da kasa a bayyane take: Wajibin ne a kare rayuwa da lafiyar fararen hula da abubuwan da ba na soji ba a kowane hari,” in ji sanarwar da Turk ya fitar.

Ya ce, datse Gaza da Isra’ila ta yi ya kara jefa Falasdinawan cikin halin ha’ula’i musamman wajen samun agaji da motocin daukar marasa lafiya, a daidai lokacin da ake samun karuwarn mutanen da hare-haren Isra’ila suka shafa.

Ya ci gaba da cewa “Dokar kasa da kasa ta haramta kowace irin tarewar da za ta jefa rayuwar fararen hula ko hana isar abubuwan bukata na rayuwa a gare su.

“Sanarwar ta ci gabad a cewa duk matakin hana zirga-zirgar jama’a da kayayyaki, laifi ne da zai iya jawo horo mai tsanani, idan babu lalurar yin hakan.