✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojojin Amurka sun kai samame wani rukunin gidaje a Abuja

An bukaci mazauna yankin da su kasance cikin taka tsan-tsan.

Sojojin Amurka da jami’an Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS, sun kai samame a rukunin gidaje na Trademore da ke unguwar Lugbe a Abuja, babban birnin Najeriya.

An kai farmakin ne a daidai lokacin da ake kara fargaba kan yiwuwar harin ta’addanci a babban birnin kasar.

Amurka da Birtaniya sun yi gargadin yiwuwar kai harin ta’addanci a Abuja, musamman kan gine-ginen gwamnati da wuraren ibada da makarantu da dai sauransu.

Gwamnatocin Australia, Ireland da Canada su ma sun nuna fargaba kan yiwuwar barazanar harin ta’addanci a babban birnin Najeriya.

A yayin farmakin da aka kai a rukunin gidaje na Trademore, an takaita zirga-zirga gaba daya, yayin da jami’an tsaro ke farautar masu tayar da kayar bayan.

Wata sanarwa da hukumar gudanarwar rukunin gidajen ta fitar, ta bukaci mazauna yankin da su kasance cikin taka tsan-tsan.

Rahotanni sun bayyana yadda jami’an tsaro ke bakin kokarinsu wajen ganin an dakile munanan hare-haren da ‘yan ta’adda masu biyayya ga kungiyar IS a Yammacin Afirka ta ISWAP suke kokarin kai wa Abuja da kewaye.

Gano shigar ‘yan ta’addan Abuja ya biyo bayan wani gagarumin aikin leken asiri ta sama da samamen da sojojin Najeriya suka yi a Jihar Borno.

An fatattako ’yan ta’addan ne daga Jihar Borno mai iyaka da Chadi da Nijar da Kamaru da dazuzzukan Alagarno da Sambisa a Arewa maso Gabas, kari a kan hare-haren bama-bamai a yankunan da ke da dazuzzuka a sassan kasar.