✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji za su rushe duk gidan da aka boye ’yan sara-suka a Jos

Sakamakon yadda ’yan sara-suka suke addabar al’ummar garin Jos fadar Jihar Filato da ayyukan ta’addanci, Kwamandan  Rundunar Samar da Zaman Lafiya a Jihar Filato (OPSH),…

Sakamakon yadda ’yan sara-suka suke addabar al’ummar garin Jos fadar Jihar Filato da ayyukan ta’addanci, Kwamandan  Rundunar Samar da Zaman Lafiya a Jihar Filato (OPSH), Manjo Janar Rogers Nicholas ya yi gargadin cewa rundunarsa za ta shiga duk wani gida da ’yan sara-suka suka shiga suka buya a garin Jos, domin ganin ta kamo su matukar aka tabbatar cewa babu mata da kananan yara a gidan kuma za ta rushe gidan da ake boye ’yan sara-sukar. 

Kwamandan ya yi gargadin ne a wajen wani taro da ya yi da shugabannin addinai da na al’umma da sauran masu ruwa-da-tsaki na garin Jos, kan yadda za a magance ayyukan ta’addancin ’yan sara-suka a birnin.

 Janar Nicholas ya ce daukar matakin ya zama wajibi ga rundunarsa ne ganin irin yadda ’yan sara-sukar suka addabi jama’a a garin Jos. Ya ce binciken tsaro da aka gudanar an gano cewa mafiya yawa daga cikin kungiyoyin ’yan sara-sukar da suka addabi jama’a a garin Jos, ba ’yan Najeriya ba ne. 

“Daga yanzu idan jami’anmu suka biyo ’yan sara-suka, suka shiga wani gida idan har ba a fito mana da su ba, nan take za mu rushe gidan. Domin ba za mu amince ’yan sara-sukar, su ci gaba da ta’addancin da suke aikatawa ba. Kuma ba za mu amince ’yan sara-sukar, su sake mayar da mu baya ba, kan zaman lafiyar da aka samu a jihar nan,” inji Janar Nicholas.

Kwamandan ya ce babban kalubalen da suke fuskanta a wannan aiki, shi ne idan sun kama ’yan sara-sukar, suka mika wa ’yan sanda aka gurfanar da su a gaban kotu, daga bisani akan bayar da belinsu.

Ya ce’yan sara-sukar, suna daukar miyagun makamai tare da aikata miyagun ayyuka kamar far wa jama’a da sace-sacen jama’a da aikata fyade. Ya ce sun hada hannu da sauran jami’an tsaro da ke jihar domin magance ayyukan ’yan sara-sukar.

Kwamandan ya gargadi iyayen yara da shugabannin al’umma da ke garin Jos, su dauki matakan tura ’ya’yansu zuwa makarantu maimakon barinsu suna yawace-yawace.

Tun da farko a wajen taron shugabannin addini da na al’umma da sauran masu ruwa-da-tsaki a garin Jos, sun goyi bayan rundunar kan daukar wannan mataki na kama ’yan sara-sukar, a kokarinta na magance ayyukan ta’addancin da suke aikatawa a garin.