Sojoji sun yi wa Shugaban Jamhuriyyar Nijar, Mohamed Bazoum juyin mulki a daren nan.
Kafofin watsa labarai sun ruwaito sojojin na sanar da kifar da Gwamnatin Bazoum a gidan Talabijin na kasar.
- ’Yan bindiga sun harbe sojoji 7 da manoma 22 a Zamfara
- Sojojin Nijar sun fatattaki magoya bayan Bazoum daga kofar fadar Shugaban Kasa
Sojojin sun ce sun rusa Kundin Tsarin Mulkin Kasar, sun kuma dakatar da dukkan hukumomi tare da rufe iyakokin kasar da ke Yammacin Afirka.
Gabanin faruwar wannan lamari, Majalisar Dinkin Duniya da Amurka da Kungiyar Kasashen Turai EU da Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS sun yi Allah-wadai da abin da ke faruwa a Jamhuriyar Nijar.
Hakan dai ya biyo yadda wasu dakaru da ke tsaron Fadar Shugaban Kasa suka tsare Shugaba Mohammed Bazoum a wani yunkuri na juyin mulki, yayin da ’yan kasar suka fara gudanar da zanga-zanga.
Masu goyon bayan Bazoum ne suka doshi fadar shugaban kasar, amma dakarun da suka yi garkuwa da shi suka tarwatsa su da harbin bindiga.
Aminiya ta ruwaito cewa tun da safiyar wannan Larabar ce sojojin da ke tsaron Fadar Shugaban Nijar suka tsare daukacin hanyoyin shiga Fadar Gwamnatin da ke birnin Yamai.
Shugaba Bazoum wanda amini ne na kut da kut da Faransa, an zabe shi ne a shekarar 2021 domin jagorantar kasar da ke fama da talauci, yayin da take da tarihin samun rashin zaman lafiya.
Nijar ta gamu da juye-juyen mulki har sau hudu tun bayan karbar ’yancinta daga Faransa a shekarar 1960 baya ga dimbin yunkuri iri-iri da aka yi na kifar da wasu shugabannin kasar daga kan karaga.
Tun daga shekarar 2020, an samu akalla juyin mulki har sau biyar a wasu kasashen yammacin Afirka.