✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojojin Nijar sun fatattaki magoya bayan Bazoum daga kofar fadar Shugaban Kasa

Dakarun sojin kasar sun tsare shugaba Bazoum a fadar shugaban kasar

Sojojin Nijar sun tarwatsa wasu magoya bayan Shugaban Kasar, Mohammed Bazoum, da suka doshi fadar shugaban, da harbin bindiga.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da aka shiga halin rashin rashin tabbas bayan yunkurin juyin mulkin da jami’an tsaron Fadar Shugaban suka yi da safiyar Laraba.

Tuni dai Majalisar Dinkin Duniya da Amurka da Kungiyar Kasashen Turai (EU) da Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS) suka yi Allah-wadai da abin da ke faruwa a kasar.

A cikin kakkausan lafazi, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Gutteres ya caccaki yunkurin juyin mulkin da ya bayyana a matsayin zagon-kasa ga gwamnatin dimokuradiyya da kuma zaman lafiyar a kasar.

Guterres, ya yi kira ga dukkanin masu hannu a wannan yunkurin na juyin mulki da su janye matakinsu domin kare dokokin kundin tsarin mulki.

Ita ma fadar White ta shugaban Amurka ta ce tana cikin damuwa kan abin da ke faruwa a Nijar, inda ta yi tur da tsare shugaba Bazoum tare da jan kunnen dakarun suka tsare shi da su gaggauta sakin sa domin kauce wa tashin hankali a kasar.

Haka nan Kungiyar Kasashen Turai ta EU ta bakin shugaban kula da manufofinta na ketare, Josep Borrell ta caccaki abin da ta kira yunkurin wargaza demokuradiya da kuma barazana ga zaman lafiyar Nijar.

Tuni Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS ta nada shugaban Benin, Patrice Talon domin jagorantar wata tawaga ta musamman da aka kafa domin shiga tsakanin bangarorin biyu da zummar sasanta rikicin na juyin mulki.

ECOWAS ta nanata cewa, ba za ta lamunci ci gaba da samun juye-juyen mulki ba a kasashen Afrika ta yamma.

Shugaba Bazoum wanda amini ne na kut da kut da Faransa, an zabe shi ne a shekarar 2021 domin jagorantar kasar da ke fama da talauci, yayin da take da tarihin samun rashin zaman lafiya.

Nijar ta gamu da juyim mulki har sau hudu tun bayan karbar ’yancinta daga Faransa a 1960 baya ga dimbin yunkuri da aka yi na kifar da wasu shugabannin kasar.

Tun daga 2020, an samu akalla juyin mulki har sau biyar a wasu kasashen yammacin Afrika.

A ranar Laraba ne aka wayi gari sojojin fadar gwamnatin Nijar suka tsare shugaba Bazoum a wani yunkuri na juyin mulki.