Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun yi raga-raga da wasu sansanonin ’yan ta’addan Boko Haram/ISWAP guda 24 a dajin Sambisa da ke Arewa maso Gabashin kasar nan.
Sun sami nasarar ce a wasu munanan hare-hare da suka kai a dajin karkashin dakarun runduna ta musamman ta 402, a karkashin rundunar Operation Hadin Kai kashi na biyu na hamada.
- 2023: Gwamnan Jigawa ya sayi fom din takarar Shugaban Kasa a APC
- ‘Cin zarafin mata na karuwa a kafofin sadarwa na zamani a Najeriya’
A sakamakon haka, sojojin sun sami fatattakar sansanonin ’yan ta’addan da ke Karamar Hukumar Bama a Jihar Borno.
Wani jami’in leken asiri ya shaida wa Zagazola Makama, kwararre kan yaki da tayar da kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a tafkin Chadi, cewa sansanonin sun hada da na Mantari, Gapchari, Ngalmari, Malumbori, Kyautari, Malmatari, Kanari, Kajimari, Ngauramari da Yusufari da dai sauransu.
Masanin harkokin tsaron ya lissafa wasu da suka hada da Karimi, Jaltawa, Bula Galda, Yale, Kashi, Shigabaja, Dole, Chingori, Ukcha, Dalbo Jibrin, Dagumba Zainabe, Dagumba Shettimari, Yerimari da kuma Amchile.
Ya kara da cewa a yayin farmakin na hadin gwiwa, da dama daga cikin ’yan ta’addan da suka hada da wani babban kwamanda, Adamu Ngulde, sun gamu da ruwan harsasai a hannun rundunar sojojin, lamarin da ya tilasta wa da dama daga cikinsu mika wuya yayin da mata da yara sama da 900 suka sheka lahira.
Majiyar sojojin ta ce wasu daga cikin ’yan ta’addan sun gudu sun bar makamai da kayayakinsu yayin da aka kwashe wasu daga cikinsu wadanda suka kubuta daga farmakin sojoji zuwa garuruwan Zangiri, Koroshirili Ali Kanzari, Bashari da Kardari, wurin da za a yi amfani da shi wajen jinyar mayakan da suka samu raunuka. .
A kwanakin baya dai Manjo Janar Christopher Musa, Kwamandan rundunar ta Operation Hadin Kai, ya bayyana a cikin wata hira da ya yi da manema labarai cewar sun yi nasarar kawar da yankin Sambisa da Timbuktu daga hannun ’yan ta’addan.
Ya ce “Mun wuce bayan Gwoza zuwa Sambisa tare da share yankin gaba daya. Wannan shi ne abin da zan iya fada muku a yanzu. Duk abin da wadannan ’yan ta’addan suke yi a halin yanzu an ci galaba akan su.
“Mun fatattake su daga dukkan sansanoninsu. Haka nan harin ya shafi yankin Timbuktu kuma mun sami ci gaba sosai. Muna godiya da irin gudunmawar da shugabanmu ya bayar domin yanzu an kara bamu karfin kayan aiki. Kuma da yardar Allah muna samun ci gaba,” inji Kwamandan.