✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojoji sun yi juyin mulki a Myanmar, sun tsare Aung San Suu Kyi

Sojojin sun kuma tsare fitacciyar 'yar siyasar kasar, Aung San Suu Kyi da ma wasu kusoshin gwamnatin kasar

Sojojin kasar Myanmar sun karbe iko da kasar Myanmar (Burma) bayan wani juyin mulki da sanyin safiyar Litinin tare da kakaba dokar ta-baci a duk fadin kasar.

Sun kuma tsare jagora kuma fitacciyar ’yar siyasar kasar, Aung San Suu Kyi da ma wasu kusoshin gwamnatin kasar a wani samame da suka yi da sanyin safiyar Litinin.

Matakin dai ya biyo bayan ci gaba da zaman dar-dar da ake yi a kasar kan takaddamar da ta biyo bayan zaben watan Nuwambar bara, wanda jam’iyya mai mulki ta lashe da gagarumin rinjaye.

Tuni dai sojojin a wani jawabi da suka watsa ta kafafen watsa labaran kasar suka sanar da sunan Janar Min Aung Hlaing a matsayin wanda zai ci gaba da jagorantar kasar na tsawon shekara daya mai zuwa.

Kakakin jam’iyyar kasar mai Mulki ta NLD, Myo Nyunt ya ce tun da sanyin safiyar Litinin ne dai sojojin suka tsare Aung San Suu Kyi, Shugaban Kasa, Win Myint da sauran jagororin gwamnati.

To sai dai Misis Suu Kyi ta yi kira ga al’ummar kasar da su yi Allah-wadai da juyin mulkin ta hanyar fitowa su yi zanga-zanga.

Tuni dai shugabannin kasashen duniya da dama suka fara Allah-wadai da juyin mulkin tare da kiran shi a matsayin wani mummunan koma baya ga dimokradiyya.