Sojojin Najeriya sun tsinto daya daga cikin ’yan matan Chibok din da aka sace a garin Ngoshe da ke Jihar Borno, tare da jaririnta.
An tsinci matar ce mai suna Mary Ngoshe a sumamen da runduna 26 ta Sojojin ta kai ranar 14 ga watan Yunin 2022 a yankin.
- Babu me yi wa Buhari katsa-landan a mulkinsa — Fadar Shugaban Kasa
- Za a yi zaman makokin kwana 3 kan kisan mutum 50 a Burkina Faso
Mary dai ana kyautata zaton guda ce daga ’yan matan Chibok 276 da ’yan Boko Haram suka sace a makarantar Sakandiren Chibok da ke Jihar ta Borno ranar 14 ga watan Afrilun 2014.
Bayan da guda 50 daga ciki suka tsere daga hannun ’yan Boko Haram din, daga baya an ceto wasu guda 100.
Wasu daga cikinsu da aka gano dai an same su da jarirai kamar na Mary.
A wata sanarwa da rundunar sojin ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Laraba, ta ce yayin sintiri a Karamar Hukumar Gwoza da ke Jihar ta Borno, ta tsinyo Mary Ngoshe da jaririnta.
Harin chibok din dai shi ne irinsa na farko a wancan lokacin a Najeriya, wanda kuma ya bude kofa ga sace-sacen daliban da aka yi a makarantunsu a sassan kasar daban-daban.