✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun tafka ƙazamin artabu da Bello Turji a Sakkwato 

Mazauna yankin sun yi fatan musayar wutar ta yi sanadin kawo ƙarshen Bello Turji.

Sojoji da maharba sun yi musayar wuta da ƙasurgumin ɗan bindiga, Bello Turji, a garin Gatawa da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Birni a Jihar Sakkwato.

Wasu mazauna Gatawa sun shaida wa Aminiya cewa an fara musayar wutar ne da misalin ƙarfe 6 na safiyar ranar Talata.

Wani daga cikin majiyoyin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ‘yan bindigar sun yi ƙoƙarin kai hari garin, amma sojoji da maharba suka daƙile su.

“Muna tunanin cewa Bello Turji ne da kansa ya jagoranci kai harin. An fara musayar wuta da ƙarfe 6 na safe, kuma har yanzu (ƙarfe 2:45 na rana) da nake magana da kai, ɓangarorin biyu na ci gaba da musayar wutar.

“Muna cikin tsananin firgici domin ba wanda ya san abin da zai faru nan gaba. Garin ya yi shiru; babu wani motsi. Ba a shiga, ba kuma fita a garin a halin yanzu.

“Babu wanda zai iya ba ka cikakken bayanin abin da ke faruwa tsakanin sojojin da ‘yan bindigar a yanzu. Sai bayan an gama artabun za mu iya samun cikakken labari.

“Muna addu’a sojoji su yi nasara a kan ‘yan bindigar, kuma muna fatan Bello Turji zai kasance cikin waɗanda aka kashe a yayin artabub.”

Wani mutum wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce, “Wannan shi ne mafi tsananin faɗa da muka taɓa gani tsakanin sojoji da ‘yan bindiga a yankin nan.

“Ba mu taɓa ganin irin wannan faɗa va a cikin garin nan. Muna fata wannan zai zama ƙarshen Bello Turji.

“Muna fatan a turo ƙarin sojoji don tallafa wa waɗanda suke faɗan a halin yanzu. Na tabbata ’yan bindigar ma za su kira ƙarin ’yan kungiyarsu don su taimaka musu.”

Duk da cewa ana zargin Turji na rayuwa ne a daji a Ƙaramar Hukumar Shinkafi ta Jihar Zamfara, yankin da ya mamaye har zuwa Sabon Birni, Isa da kuma Goronyo a Jihar Sakkwato.