✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun sake tarwatsa sansanin mayakan ISWAP a Borno

Shalkwatar tsaro ta kasa ta ce a ci gaba da ruwan wutar da take yi kan ‘yan ta’adda a yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya ta…

Shalkwatar tsaro ta kasa ta ce a ci gaba da ruwan wutar da take yi kan ‘yan ta’adda a yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya ta sami nasarar tarwatsa wani sansanin kungiyar ISWAP a jihar Borno.

Jami’in da ke kula da samar da bayanai kan ayyukan rundunar, Manjo Janar John Enenche ne ya bayyana haka a wata sanarwa a Abuja ranar Laraba.

Ya ce sansanin da aka tarwatsa a  garin Tumbun Barorowa yake, dab da yankin Tafkin Chadi na jihar Borno.

Manjo Janar Enenche ya ce rundunar tsaro ta Operation Lafiya Dole karkashin shirin ‘Operation Wutar Tabki’ ce ta kai harin a ranar 19 ga watan Oktoban da muke ciki.

Ya ce harin ya biyo bayan samun wasu bayanan sirri ne da suka nuna cewa ana amfani da wurin a matsayin sansanin bayar da horo ga mayakan na ISWAP.

Enenche ya ce, “Jiragen hangen nesanmu sun kai ga gano wasu gine-gine a wasu dazuka da ‘yan ta’addar ke amfani da shi wajen boye makamansu.

“A sakamakon haka, jirgin yakin Rundunar Sojin Saman Najeriya da bama-bamai da rokokin yakinmu sun sami nasarar tarwatsa wurin sakamakon wutar da ta tashi daga bisani kuma bakin hayaki ya turnuke wurin.

“Mun sami nasarar kashe mayakan ISWAP da dama a harin,” inji Enenche.