Rundunar Sojin Najeriya ta ce za ta ba da tukwicin Naira miliyan biyar kan kowane dan ta’adda ga duk wanda ya taimaka mata da muhimman bayanan da za su kai ga kama wadanda take nema ruwa a jallo su 19.
Rundunar ta ce ta bullo ta wannan hanyar ce domin ba ta damar cika aikinta na maido da zaman lafiya a fadin kasar nan.
- An kori karamin Ministan Kudin Ghana saboda cin hanci
- ’Yan bindiga sun kashe basarake da mai juna-biyu a Imo
Sai dai wasu mazauna Jihar Zamfara sun bayyana shakkunsu kan wannan mataki da rundunar ta dauka, inda suke da shakku a kan ko hakar rundunar za ta cim ma ruwa.
Kazalika, sun yi mamakin yadda sojojin suka kasa daukar matakin ayyana neman ‘yan ta’addar ruwa a jallo a baya sai a yanzu.
A ranar Litinin, Babban Ofishin Tsaro ya saki sunayen kwamandojin ‘yan ta’addar su 19 wadanda suka fitini yankin Arewa.
Jerin sunayen ‘yan bindigar da rundunar ta fitar ta bakin Daraktan Sashen Yada Labarai, Manjo-Janar Jimmy Akpor, sun hada da: Sani Dangote da Bello Turji Gudda da Leko da Dogo Nahali da Halilu Sububu da Nagona da Nasanda da Isiya Kwashen Garwa da Ali Kachalla (Ali Kawaje) da kuma Abu Radde.
Sauran su ne; Dan-da da Sani Gurgu da Umaru Dan Najeriya da Nagala da Alhaji Ado Aliero da Monore da Gwaska Dankarami da Baleri, sai kuma Mamudu Tainange.
Da yake zantawa da wakilinmu, wani mazaunin Zamfara, Mustapha Shinkafi, ya ce gamawa da ‘yan ta’addar ya kamata sojojin su yi maimakon ayyana neman su ruwa a jallo.
Ya ce ‘yan bindigar sun dade suna cin karensu babu babbaka a sassan Zamfara da kewaye.
Don haka ya ce, “Ayyana neman ‘yan ta’addar ruwa a jallo ba zai suya komai ba. Abu daya da zai taimaka wajen inganta tsaron kare rayuka da dukiyoyin jama’a shi ne, gamawa da ‘yan ta’addar baki daya.”
Haka shi ma Musa Hassan, ya ce a baya ‘yan sanda sun ayyana neman jagoran ‘yan ta’adda, Ado Aleiro, ruwa a jallo tare da cewa za su ba da tukwici ga duk wanda ya gano shi, ba da jimawa ba ya jagoranci kai mummunan hari a kauyen Kadisau, cikin Karamar Hukumar Faskari a Jihar Katsina.
“Tun daga wancan lokaci Ado Aliero ke zirga-zirgarsa ba tare da wata takura ba, har da sarauta ma aka ba shi a kauyen Yandoto a watanni baya.
“Ni ma ina ra’ayin gamawa da su shi ne mafita maimakon nemansu ruwa a jallo,” in ji Hassan.