Dakarun rundunar Soji ta OPWS, sun bindige ’yan ta’adda a wata musayar wuta da suka yi ranar Lahadi da dare a yankin Adaka na Karamar Hukumar Makurdi, Jihar Binuwai.
Mazauna sun shaida wa Aminiya cewa, shigar ’yan bindigar yankin na Adaka don yin fashi ke da wuya sai sojojin suka kawo wa wurin dauki.
- Yadda masu karbar haraji suka ‘hallaka’ wani direba
- Matsalar tsaro: Kusoshin PDP sun bukaci a tsige Buhari
- Mutum miliyan 17 sun fara kada kuri’a a zaben sabon shugaban kasar Ghana
Majiyarmu ta ce mazauna kauyen ne suka sanar da sojojin yayin da suka ga gilmawar motarsu ta sintiri don su kawo musu dauki daga harin yan ta’addar.
Sun ce maharan na shiga garin da misalin karfe 8:00 na yamma suka bindige wata mata da mijinta.
Kwamandan rundunar OPWS, Manjo Janar Adeyemi Yekini, ya tabbatar cewa jami’ansu sun yi arangama da ’yan ta’addar a yankin na Adaka.
“Rundunarmu a shirye kuma a ankare take da yanayin tsaro, don haka za mu yi iya iyawarmu tare da hadin guiwar ragowar jami’an tsaro wurin kare lafiyar jama’a”, inji shi
Yekini, ya ce sashen yada labarai na shalkwatarsu a shirye yake a wurin karbar bayanai a kowane lokaci masu alaka da irin wannan.