✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojoji sun ragargaji ’yan Boko Haram a Gwoza

Ana gab da shan ruwa suka far wa garin, nan take kuma sojoji suka yi musu kaca-kaca

Dakarun sojin Najeriya sun yi wa mayakan Boko Haram kaca-kaca, ana gab da bude baki agarin Gwoza na Jihar Borno.

Mayakan na Boko Haram sun kwashi kashinsu a hannun sojojin ne bayan sun yi yunkurin kutsawa cikin garin a yayin da ake shirye-shiryen shan ruwa.

Nan take sojojin suka fatattake su, inda suka kuma suka ce kafa me na ci ban ba ki ba.

Wani mazaunin garin, Ibrahim Muhammad Turaki ya tabbatar wa Aminiya cewa maharan “sun yi kokarin shiga cikin garin, amma da taimakon Allah sojoji sun dakile kokarin nasu kuma tuni an kora su zuwa bayan dutse.”

A cewarsa, sun yi buda baki da harbe-harben bindiga, amma babu wani bayani game da asarar rai.

Ibrahim ya ce maharani sun bullo wa garin Gwoza ne ta bangaren Yamma ta hanyar Dambuwa.

A cewarsa, zuwa karfe 7:30 na magariba komai dai ya lafa, amma yana kyautatata zaton sojoji za su cimma maharan su karasa su.

A ’yan kwanakin nan, kungiyar ta kara kaimi wurin kai hare-hare da kwace garuruwa a Jihar ta Borno.

%d bloggers like this: