Rundunar sojin Najeriya ta mika Lydia Simon ’yar makarantar Chibok da aka ceto tare da ’ya’yanta uku ga Gwamnatin Borno domin mika ta ga iyalenta.
Kwamandan rundunar Operation Hadin Kai na Arewa maso Gabas, Manjo-Janr Waidi Shuaibu, ne ya bayyana hakan a Maiduguri.
Ya ce dakarun sun ceto matar mai dauke da cikin wata shida tare da ’ya’yanta uku a ranar Laraba 17 ga watan Afrilu a Karamar Hukumar Gwoza ta jihar.
Shuaibu ya ce ita ce mai lamba 18 a cikin ’yan matan da sojojin Najeriya suka ceto.
A cewarsa, an yi kokari da dama a kasashen duniya ganin an dawo da ’yan matan cikin koshin lafiya da kuma sada su ga iyalansu.
Shi ma da yake magana, Birgediya Abubakar Haruna, Mukaddashin (GOC), shiyya ta 7, ya ce dalibar ta samu kulawar jinya da sauran kulawa da ta dace tun bayan da aka ceto.