Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta damka wa Gwamnatin Jihar Borno tsoffin ’yan Boko Haram 565 da suka tuba.
Kakakin Hedikwatar Tsaro ta Najeriya, Birgediya Benard Onyeuko, ya ce an mika wa gwamnatin jihar tsoffin mayakan kungiyar ne domin ci gaba da lura da su bayan daukar bayanansu.
- Tsohon dan bindiga da gwamnatin Katsina ta dauka aiki ya koma gidan jiya
- Kotu ta sa a duba kwakwalwar Sheikh Abduljabbar
Da yake sanar da hakan a Hedikwatar Tsaron a ranar Alhamis, Birgediya Onyeukoya ce “’Yan Boko Haram 565 tare da kwamnandojinsu uku, da amir-amir hudu da Nakib-nakib biyar da kwarraru wajen satar shanu su biyar da iyalansu duk sun mika wuya kuma an damka su ga Gwamnatin Jihar Borno a Maiduguri domin ci gaba da gudanar da al’amarinsu bayan daukar cikakkun bayanansu.”
Ya kara da cewa daga ranar 12 ga Agusta zuwa 1 ga Satumba, 2021, “’Yan Boko Haram akalla mutum 5,890 da suka kunshi mayaka da kwamandojin kungiyar da iyalansu ne suka mika wuya ga sojoji a Arewa maso Gabas.”
Onyeuko ya ce ’yan Boko Haram din sun mika wuya ne ga sojojin Rundunar Operation Hadin Kai da ke yakar kungiyar a yankin Arewa maso Gabas.
Sojojin sun kuma kwace bindigogi na musamman guda 52 da gurneti-gurneti da bindigogi masu harba gurneti da harsasai 1,977 da kwanson harsasan bindigogi kirara AK-47 da FN, da bindigogin ’yan sanda da sauransu a hannun tubabbun ’yan Boko Haram din.
Kakakin Hedikwatar Tsaron ya kara da cewa wasu mutum bakwai da ke hada baki ko kai bayanai ko yi wa kungiyar jigilar kayayyaki sun shiga hannu, an kuma mika su ga hukumomin da suka dace domin su fuskanci hukunci.