✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kwato mutum 6 da aka yi garkuwa da su a Kaduna 

Gwamnatin Jihar ce ta tabbatar da haka a wata sanarwa ranar Litinin

Dakarun sojin Najeriya sun kubuto mutane 6 da ‘yan bindiga su ka yi garkuwa da su a jihar Kaduna.

Dakarun sun kubutar da mutanen ne a yayin wani aikin sintiri da suke yi a yanki Kagon Kadi da ke karamar hukumar Chikun ta jihar.

Kwamishinan Tsaro da Al’amuran Cikin Gida na jihar Samuel Aruwan ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya sa wa hannu a ranar Litinin, a garin Kaduna.

Kwamishinan ya ce, daga bayanan da ya ke samu daga filin daga, sojojin da ke sintiri, sun bude wuta kan ‘yan bindigan ne a kokarin da su ke yi na kakkabe ‘yan bindigan da su ke boye a dazukan Kagon Kadi da Labi, da kuma bakin Kogin Udawa.

’Yan bindigan sun tsere sakamakon fin karfinsu da sojojion suka yi, a inda su ka bar wasu mutane 6 da su ke garkuwa da su a sansaninsu.

 Sanarwar ta ce gwamnan jihar, Nasir El-Rufa’i ya yi murna tare da jinjina wannan kokari na dakarun sojin.