✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kwato mutum 14 da aka yi gurkuwa da su a Kaduna

Sojoji sun kashe wani dan bindiga sannan suka ceto mutum 14 da aka yi garkuwa da su a Jihar Kaduna.

Sojoji sun kashe wani dan bindiga sannan suka ceto mutum 14 da aka yi garkuwa da su a Jihar Kaduna.

Sojojin Rundunar Operation Whirl Punch sun hallaka dan bindigar ne a musayar wuta a lokacin samamen da suka kai wata maboyar ’yan bindiga a yanin Tukurua da ke Karamar Hukumar Chikun ta jihar.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya sanar a safiyar Asabar cewa, “mutum 14 da aka ceto sun hada da maza tara da mata biyar, kuma an tafi duba lafiyarsu kafin a mika su ga iyalansu.”

Aruwan, wanda ya ce sojojin sun lalata wasu maboya biyu na ’yan bindiga ya bayyana jinjinar Gwamna Nasir El-Rufai gare su, bisa hazaka da kwarewar da suka nuna wajen ceto mutanen da ke hannun ’yan bindigar ba tare da komai ya same su ba.