Rundunar Sojin Najeriya ta samar da cewa dakarunta sun kashe ’yan ta’adda 1,770, sun kama wasu 3,070 a yankin Arewa maso Yamma a shekaru uku da suka gabata.
Rundunar ta kuma yi nasarar ceto mutane fiye da 2,515 da harin ya rutsa da su ta hanyar gudanar da ayyukan haɗin gwiwa a jihohin da lamarin ya shafa.
Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ne ya sanar da hakan a yayin wani gangamin wayar da kan jama’a a Jihar Katsina, wanda aka gudanar ga mazauna ƙananan hukumomin Batsari da Dutsin-Ma.
Janar Musa ya ce, sun kuma ƙwato sama da makamai 1,000 da alburusai 12,000 a hare-haren da suka kai a jihohin Arewa maso Yamma guda biyar, wato Katsina, Kaduna, Kebbi, Sokoto, da Zamfara, tare da daƙile ayyukan ta’addanci.
- Magidanci ya kashe kansa saboda mutuwar matarsa a Neja
- Janyewar sojoji ke ba Boko Haram damar ƙwace yankuna —Zulum
“Sojoji na yin iya ƙoƙarinsu wajen yaƙi da matsalar tsaro,” in ji shi, yana mai jaddada cewa nasarorin da aka samu wani ɓangare ne na ƙoƙarin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin ƙasar.
Aikin na da nufin ƙarfafa haɗin gwiwar al’umma da shugabannin sojoji da mazauna yankuna a wani yunƙuri na ƙulla alaƙa mai ƙarfi da ƙarfafa sanya ido a tsakanin al’ummomi.
A yayin taron wayar da kan al’umma, Janar Musa ya tunatar da mazauna yankin cewa wanzar da zaman lafiya nauyi ne na haɗin gwiwa. Ya kuma yi kira ga al’ummomin da su ba da rahoton abubuwan da ake zargi da kuma tallafa wa juna.
Janar Musa ya kuma bayyana cewa, a halin yanzu sojoji na sake yin wani shiri domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a dukkan al’ummomin da ke kan gaba a matsalar tsaro.
Wannan yana nuna ci-gaba da sadaukar da kai ga ɗaukar matakan tsaro da barazana yayin da mazauna da yawa suka yarda da ingantaccen tsaron.
Al’umma a Batsari sun yaba da ƙoƙarin baya-bayan nan, musamman tattaunawar da aka yi da masu laifin da suka tuba, wanda ya taimaka wajen raguwar tashin hankali.
Duk da haka, wasu sun bayyana damuwarsu. Malam Lawal Rabi’u, wani mazaunin yankin, ya nuna damuwarsa kan hare-haren ’yan bindiga daga ƙananan hukumomin da ke maƙwabtaka da su inda har yanzu ba a fara aiwatar da shirin na sulhu ba.
Duk da waɗannan ƙalubalen, babban saƙon sojoji yana ba da ƙarfi da begen yin gamayya. Kiran da Janar Musa ya yi na haɗin kai inda ya ce, “Tare, za mu iya dakatar da ci gaba da tashin hankali da muryar zaman lafiya,” ya yi ƙarfi a tsakanin waɗanda suka halarta, yana mai jaddada ra’ayin cewa dawwamammen zaman lafiya ya dogara ne da haɗin gwiwar sojoji da ’yan Najeriya.