✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kashe ’yan ta’addan ISWAP 140 a watan Disamba 

An kashe su ne tsakanin 1-22 ga watan Disamban 2022

A cigaba da ragargazar ’yan ta’addan ISWAP/Boko Haram, sojojin Najeriya sun kashe jimlar mayakan kungiyar kimanin 140 a cikin watan Disamban 2022.

An kashe adadin mutanen ne a hare-haren da aka kai tsakanin ranar daya zuwa 22 ga watan, sannan kuma an ji wa wasu da dama munanan raunuka.

A cewar Zagazola Makama, kwararre kuma mai sharhi kan al’amuran tsaro a yankin Tafkin Chadi, rundunar sojan kasa da na sama na Operation HADIN KAI sun ci gaba da mamaye yankin gaba daya na ayyukansu.

Ya ce an sami nasarar ce da ayyukansu a kauyuka da garuruwa da tsaunuka da ke cikin Kananan Hukumomin Damboa da Bama da Gwoza da Konduga na jihar Borno, da kuma na Gulani da Geidam a Jihar Yobe.

A cewar Zagazola, musamman a ranar 1 ga Disamba, 2022, sojoji sun gwabza da ’yan ta’addan Boko Haram/ISWAP a Damboa ta jihar Borno.

Dakarun da ke samun goyon bayan jiragen sama sun yi artabu da ’yan ta’addan tare da kashe da dama yayin da sauran suka gudu da manyan raunuka a jikinsu.

Sojojin sun yi amfani da dabaru yaki  inda suka kwato bindigogi kirar AK47 guda shida, bindigogin FN 3, bindigogin QJC guda 2, harsashi 102 na 12.7mm, 2,152 na musamman na 7.62mm na musamman, 20 na 7.62mm NATO, bututu 1 RPG, bam 1 HEAP, 1 HEAP Bom.

Sauran makaman da aka kwato sun hada da bam da gurneti na hannu.

Sojojin sun kuma samu nasarar kwato daya daga cikin motar ’yan ta’addan tare da lalata wata motar bindiga guda daya.

Hakazalika, a ranar biyu ga Disamba, 2022, sojojin da ke sintiri na yaki sun yi karo da ‘yan ta’adda a yayin da suke yin amfani da dajin da ke wajen garin Mallam Fatori a Karamar Hukumar Abadam ta jihar Borno.

A yayin musayar wuta a wannan hari sojoji sun kashe ’yan ta’adda biyar tare da kama daya.

Har ila yau, a ranar 11 ga Disamba, 2022, sojoji sun kama kwamandojin ’yan ta’addar Boko Haram hudu a kan hanyar Gwoza zuwa Yamteke a Karamar Hukumar Gwoza ta jihar Borno.

An bayyana cewa sun tsere ne daga Sabil Huda da ke dajin Sambisa saboda tsananin ruwan bama-bamai da dakarun nasu suka yi.

Abubuwan da aka kwato daga hannun ’yan ta’adda sun hada da bindigogin AK-47 guda uku, bindiga korar G3 guda daya, da alburushi 20 na musamman na 7.62mm, harsashi guda 12 da wayoyin hannu guda biyu da tsabar kudi Naira 125,400 da sauran kayayyaki.