Hedkwatar Tsaro ta ce dakarunta sun kashe ’yan ta’adda 77 a lokuta daban-daban kuma a sassa mabambanta a Arewacin Najeriya a cikin makonni biyun da suka gabata.
Hedikwatar ta ce samamen da aka kai sun shafi yankunan Arewa maso Gabas da Arewa ta Tsakiya da kuma Arewa maso Yamma.
Daraktan Yada Labarai na hedkwatar, Manjo-Janar Musa Danmadami ne ya bayyana haka a wajen taron manema labarai ranar Alhamis a Abuja.
A cewarsa, dakarun rundunar Operation Hadin Kai masu aiki a shiyyar Arewa ta Gabas sun kashe mayakan Boko Haram/ISWAP 56 Boko, sun cafke 26 sannan sun kubutar da 59 da ke hannu ‘yan ta’addar.
Ya kara da cewa, mayakan sama sun samu nasarar hallaka ‘yan ta’adda da yawa a Gogore a mabuyarsu da ke Damboa da Tumbun Dila da Arege da sauransu a Jihar Borno.
Danmadami ya ce kimanin ’yan ta’adda 340 da suka hada iyalansu suka mika wuya ga sojoji a wurare daban-daban.
Ya ce sun kwace tarin bindigogi da alburusai mallakar NATO da jarkokin fetur da sauransu yayin samamen.
Kazalika, ya ce kamen ya hada da wasu masu yi wa ‘yan bindigar safarar makamai da kayan masarufi.
(NAN)