Dakarun sojojin Najeriya sun kashe wasu ‘yan ta’adda hudu ne tare da ceto wasu mutum 11 da aka sace a Kaduna.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mukaddashin daraktan hulda da jama’a, Laftanar Kanar Musa Yahaya ya fitar.
- An kama ɗan bindigar Katsina yana ƙoƙarin kafa sansani a Kano
- Yadda wasan Najeriya da Afirka ta Kudu ya yi ajalin mutum 5 saboda faɗuwar gaba
Ya kara da cewa dakarun sun kashe mahara hudu ne yayin da wasu kuma suka tsere da harbin bindiga.
Ya ce maharan sun sace mutanen ranar 6 ga watan Fabrairu, 2024 a kauyensu da ke Masuku a Karamar Hukumar Shiroro a Jihar Neja.
A cewarsa an mika wadanda aka ceto asibiti inda likitoci suka duba su, sannan aka sada su da iyalansu.
Ya kuma yaba wa babban Kwamandan runduna ta daya da kuma Kwamandan rundunar ‘Operation WHIRL PUNCH’, Manjo Janar Valentine Okoro, kan yadda suka fatattaki maharan.
Kazalika ya yi kira ga al’ummar yankin da su kai bayanan duk mutumin da suka gani da harbin bindiga.
Ya sake jaddada aniyar rundunar na tabbatar da tsaro a jihar ta hanyar hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro.