Dakarun kasar Nijar da aka tura yankunan Gagam da Tchantchandi sun kashe mayaƙan Boko Haram da dama a wani Gumurzun a tsakaninsu.
Sojojin, karkashin rundunar haɗin gwiwa ta Multi National Joint Task Force (MNJTF) sun kuma yi nasarar ceto wasu mata daga hannun mayaƙan ƙungiyar da suka yi garkuwa da su.
- An tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza
- Gwamnan Kano: Ba da kuri’a kadai ake cin zabe ba —Alhassan Doguwa
Sojojin sun ragargaji ’yan ta’addan ne a ranar 27 ga watan Nuwamba l a yankin Ouhou na kasar Nijar, a matsayin martani ga sace wasu mata biyu da Boko Haram ta yi yankunan Dagaya da Tchantchandi.
Wata majiyar leken asiri ta shaidawa Zagazola Makama cewa, ’yan ta’addan suna ƙoƙarin tserewa ne sojojin Nijar da na Chadi suka yi gaggawar kutsawa cikinsu suka kashe da dama daga cikinsu, suka kubutar da matan da aka yi garkuwa da su.
Sojojin sun kuma kwato bindigogi ƙirar AK-47 daga hannun ’yan ta ’addan.