A ci gaba da aikinsu na yaki da ta’addanci, sojojin rundunar hadin gwiwa kasashe (MNJTF) sun kashe mayakan Boko Haram tare da kwato manyan makamai.
A ranar 18 ga Yuli, 2024, sojojin suka kai samame a kauyen Yashinti, Karamar Hukumar Nganzai a Jihar Bornon, ida suka kashe ’yan ta’adda hudu.
Sun kuma kwato bindiga kirar AK-47 guda daya da akwatunan albarusan AK-47 guda 3, da harsashi na musamman nau’in 7.62mm x 39mm.
A wani hari na daban a yankunan garuwan Gajiram, Marram, Tumtumari, Layinma, Kulunkiya, Gadayi Tumtumarida Kodayi a Karamar Hukumar Nganzai, sojojin sun kashe karin wasu ’yan ta’adda hudu da suke yunkurin kawo cikas ga ayyukan noma.
- Dan sanda ya harbe mahaifinsa har lahira a Borno
- Matatar Dangote: Ku zo ku saya ku yi yadda kuke so —Dangote ga NNPCL
Sojojin sun kuma kubutar da wani yaro dan shekara 10 da ’yan ta’addan suka yi garkuwa da shi, sannan suka kwato bindigogi kirar AK-47 guda biyu da akwatunan albarusai hudu, da alburusai 30 na nau’in 7.62mm da 30mm.
Dakarun na rundunar MNJTF sun kai wani hari a wata matattarar ’yan ta’adda a Karamar Hukumar Kukawa inda suka kashe ’yan ta’adda guda, suka kwato bindiga kirar AK-47 daya, da harsashi 118 nau’in 7.62mm.
Wadannan ayyuka na rundunar MNJTF na kara maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin tafkin Chadi gami da kawar da ’yan ta’adda da kwato makamansu.