Sojojin Najeriya tare da mayakan sa-kai na Civilian JTF sun kashe ’yan Boko Haram 35 suka kuma kama wani kwamandan kungiyar, Alhaji Baana a Dajin Sambisa da ke Jihar Borno.
Dakarun sun kuma lalata sansanonin ’yan ta’adda guda 12 da ke cikin dajin a wani samame da suka kai, kamar yadda Zagazola Makama, wani kwararre a fannin yaki da ta’addanci a Yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya bayyana a ranar Lahadi.
- An kama gurgu na sayar da kwaya a cikin keken guragu
- Gwamnatin Ganduje ta cancanci yabo —Sarkin Kano
Ya kara da cewa sojojin sun samu nasarar ceto wasu mata da ’yan ta’addan suka yi garkuwa da su daga dajin na Sambisa.
A cewarsa, sojojin sun kai farmakin ne a Awulari a ranar 17 ga Afrilu, 2023, suka ci gaba da fadada shi zuwa sansanonin ’yan ta’addan da ke yankin Garno/Alafa.
Samamen, a cewarsa, ba a taba ganin irinsa ba a maboyar ’yan ta’addar da ke dajin, kuma “Sojoji sun lalata sansanonin ’yan ta’adda da dama kafin su fatattake su daga Izzah da Farisu.
“Sun yi wa ’yan ta’adda da dama munanan raunuka kuma sun yi galaba a kansu bayan kazamin fadan, inda suka kashe 18 daga cikin mayakan,” in ji shi.
Ya ce daga baya sojoji sun kashe ’yan ta’adda takwas a Farisu, kuma suka kwato babura da dama da bindigogi kirar AK-47 da sauransu.
Sai dai an yi rashin sa’a wani dan CJTF ya rasa ransa.
A garin Alafa, an kashe mayakan Boko Haram uku da suka hada da Kwamandan da aka bayyana sunansa “Salafi” tare da kwato babura guda biyu.
“A dajin Ukuba kuma sojoji sun yi arba da kungiyar inda suka kashe mayaka bakwai, sauran suka tsere da raunukan harbi, amma sojojin sun kwato wata babbar mota da makamai 122.
Daga nan dakarun suka karasa zuwa Garin Glucose, inda suka kashe wasu ‘yan ta’adda biyu,
sauran suka tsere.