✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 25 a wani turnuku

Rundunar Tura ta Kai Bango ragargaji mayakan Boko Haram/ISWAP 25 a yankin Chikun Gudu da Kerenoa.

Rundunar Sojin Kasan Najeriya ta Tura ta Kai Bango, ta yi nasarar kashe Boko Haram/ISWAP 25 a yankin Chikun Gudu da Kerenoa, a Jihar Borno.

Hakan ya fito ne daga bakin kakakin Rundunar, Burgediya Mohammed Yerima, ranar Laraba a Abuja.

Yerima, ya ce sumamen ya samu hadin gwiwar sojojin rundunar Lafiya Dole da kuma dakaru na musamman, inda aka kwace makamai masu tarin yawa daga ’yan ta’addan.

Ya ce sojojin ba su damu da nasarar da suka yi ba, face maida hankali wajen dakile duk wani yunkuri na ’yan ta’adda da suka rage a yankin.

Yerima ya ce Shugaban Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Laftanar-Janar Ibrahim Attahiru, ya jinjina wa sojojin bisa namijin kokarin da suka yi.

Sai dai ya ja kunnensu da kada su yi kasa a gwiwa wajen kai farmakin da zai fatattaki ’yan ta’addan.

Ya kara da cewa Chikun Gudu da Kerenoa, kauyuka ne da ke karamar hukumar Marte a jihar Borno.

%d bloggers like this: