Rundunar Operation Sahel Sanity sojojin Najeriya ta hallaka ‘yan bindiga 80 ta kuma kwato mutum 17 da shanu 943 a jihohin Katsina da Zamfara da Sokoto.
Mukaddashin Darektan Watsa Labaran Rundunar Birgediya Benard Onyeuko ya ce ayyukan sojin a Arewa ta Yamma sun yi tasiri tare da gagarumar nasara a cikin takaitaccen lokaci.
“An kashe ‘yan bindiga 80, an kwato shanu 943, awaki da tumaki 633, an kuma tsare mutum 33 da zargin hannu a hare-haren”, inji shi.
Ya ce sojojin sun kubutar da mutum 17 da aka yi garkuwa da su, sun kwato bindigogi 24, sun tsare ‘yan leken asirin ‘yan bindiga da masu taimaka musu 14, suka kuma lalata maboyan ‘yan bindigar, ciki har da Dangote Triangle wanda ya yi kaurin suna.
Ya ce a wata daya da kafa rundunar Operation Sahel Sanity ne ta samu wadannan nasarori, kuma sojoji za su ci ga da yin sintiri a yankunan da ke fuskantar barazana tare da kai samame da kuma kwaton bauna domin hana wa maharan sukuni.
“Wadannan nasarorin da har suka kai ga ci gaban harkokin jama’a da noma sun tabbatar cewa an samu raguwar firgici a tsakanin mazauna yankunan”, inji shi.
Ayyyukan ‘yan bindiga sun jefa mazauna a jihohin Katsina da Zamfara da Kaduna cikin fargaba.
Maharan sun kashe mutane da dama sun koma gidaje bayan kwace duniyoyin jama’a da suka hada da kudi da kadarori.
Sukan yi garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa har ma su yi wa mata fyade.
Wani lokaci sukan kashe mutanen bayan karbar kudin fansa.