✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojoji sun kashe ’yan bindiga 8 a Kaduna

El-Rufai ya yaba kan irin nasarar da dakarun sojin ke samu a jihar.

Dakarun Sojin Rundunar Sharar Daji sun kashe ’yan bindiga takwas tare da kwato babura shida a wani samame a yankunan Chikun da Birnin Gwari a Jihar Kaduna.

Gwamnatin jihar ta ce sojojin sun samu nasarar ne bayan wani samame kan maboyar maharan da ke yankunan  Buruku da Birnin Gwari a jihar.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Samuel Aruwan, ya ce, “Dakarun sun bankado ’yan bindiga suka yi artabu da su.

“Sun kashe takwas daga cikinsu sannan suka kwato babura hudu da wayar hannu guda uku,” in ji shi a ranar Juma’a.

Aruwan ya ce dakarun a wani samame na daban sun kwato wasu babura biyu a hannun maharan.

Sun kuma kwato bindiga kirar AK-47 guda biyu, alburusai 52, babura uku da kuma wayoyin hannu biyu.

Kazalika, sojojin sun gano tare da lalata wata maboyar ’yan bindiga, inda suka samu bindigar mafarauta biyu, kakin sojoji da babura guda tara.

Ya ce gwamnan jihar, Nasir El-Rufai ya jinjina wa sojoin kan nasarar da suka samu.