Dakarun sojin Najeriya sun kashe ’yan bindiga biyar tare da kwato muggan makamai a yankun Birnin Gwari da Chikun na Jihar Kaduna.
Mataimakin Daraktan Yada Labarai na Rundunar Soji ta 1, Laftanar-Kanar Musa Yahaya ya ce sojojin sun kwato bindigogi kirar AK-47, abubuwan fashewa, da kuma harsasai da ababen hawa daga hannun ’yan bindigar da suka hallaka.
- Duk da umarnin ’yan sanda, dubban magoya bayan NNPP sun tarbi Kwankwaso a Kano
- NAJERIYA A YAU: Yadda Bangar Siyasa Ka Iya Dagula Lissafi A Wannan Zabe
Yahaya, ya ce, “Sojojin sun kwato yankunan Mando zuwa Sabon, Birni, Maidaro zuwa Dogon Dawa, Galadimawa, Saulawa, Farin Ruwa da kuma Polewire a Kananan Hukumomin Birnin Gawri da Chikun na jihar.”
Da yake sanar da haka a ranar Alhamis, ya bayyana cewa n gudanar da aikin ne domin samar da tsaro yayin gudanar da babban zabe cikin lumana, kuma, “A yayin samaen, sojoji sun kashe ’yan bindiga biyar tare da kwato babura 10 daga hannun hannunsu, yayin da wasu babura da dama suka kone.
“Sauran abubuwan da sojojin suka kwato sun hada da bindiga kirar AK-47 guda biyu, abubuwan fashewa guda biyar, wayoyin hannu guda biyu da kuma harsasai.”
A cewarsa, “Dakarun Runduna ta 1 da kuma rundunar sojin sama ta Operation Whirl Punch sun yi wa ’yan bindiga da sauran masu aikata laifuka a Jihar Kaduna luguden wuta inda cikin sa’o’i 48 aka murkushe ’yan bindigar.”
Yahaya, ya ce Kwamandan Runduna ta 1, Manjo-Janar Taoreed Lagbaja, ya bayyana jin dadinsa da jinjinarsa bisa yadda dakarun suka gudanar da wannan samame.