✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kashe ’yan bindiga 40 a dajin Kaduna da Sakkwato

Sojoji sun dauki mako biyu suna yi wa ’yan ta’adda luguden wuta a jihohin biyu.

Dakarun sojin sama da hadin gwiwar rundunar Operatoin Hadarin Daji sun kashe ’yan bindiga sama da 40 tare da kone maboyarsu a hare-haren da suka kai musu a cikin mako biyu.

Sojojin sun kashe ’yan ta’addar ne a hare-haren da rundunar ta kaddamar a kan maboyar ’yan bindiga a dajin Kwaga da ke Karamar Hulumar Birnin Gwari a Jihar Kaduna.

Mukaddashin Daraktan Yada Labarai na Hedikwatar Tsaron Najeriya, Birgediya Benard Onyeuko, ya ce, “Rundunarmu ta hallaka ’yan bindiga tare da kone maboyarsu kamar yadda binciken irin asarar da aka yi musu a wuraren nasu ya tabbatar.”

Wannan na kunshe a cikin sanarwar da Birgediya Onyeuko ya fitar a yayin gabatar da irin nasarorin da rundunar ke samu a ranar Alhamis 14 ga watan Oktoba.

Ya kara da cewa a dajin Mashema, Yanfako, Gebe da Gatawa na kananan hukumomin Isaa da Sabon Birni na Jihar Sakkwato ma, sojoji sun yi nasarar kashe ’yan bingigar da dama tare da kama wasu.