A ci gaba da fatattakai bata gari a yankin Arewa maso Yamma, sojoji sun bindige ’ya binidga 100 tare da tsare wasu 148 tare da kwato mutum 107 a hannunsu.
Rundunar dakarun tsaro ta Operation Sahel Sanity a yankin ta ce ta kwace bindigogi 143 da harsasai 3,261 daga ’yan bindigar wadanda aka kama shida daga cikin masu yi musu fasakwaurin makamai.
- Sojoji sun kara cafke ’yan Darul Salam 190 a Arewa
- Gwamnati ta ba da tallafin tirelan hatsi 116 a Bauchi
Mukaddamin Kakakin Rundunar, Birgediya Benard Onyeuko, ya ce masu yi wa ’yan fashi daji leken asiri 20 da masu yi musu safarar abinci 32 sun shiga hannu.
A jawabinsa a Babban Sansanin Soji da ke Faskari, Jihar Katsina babban hafsan ya ce sojojin sun cafke mutum 13 da ke sayar da shanun sata a Jihar da masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba guda 315 dauke da harmtattun makamai a Jihar Zamfara.
Rundunar ta ce ta kwato shanu 3,884 da tumaki 1,627 daga hannun barayin daji a jihohin Katsina da Kebbi da Sokoto da kuma Zamafara.
Sun kuma tarwatsa sansanoni 81 na ‘yan fashin daji ciki har da maboyar hatsabinin dan fashin daji da ake kira Dangote a Jihar Katsina.
Ya ce dakarun suka dakile hare-hare ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane guda 128 a yankin.