✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojoji sun kashe wani babban kwamandan Boko Haram da wasu mayaka 14 a Borno

An kashe su ne lokacin da sojoji suke sintiri

A wata arangama da suka yi da ’yan kungiyar Boko Haram a yankin Mafa cikin Jihar Borno, sojojin Najeriya sun yi nasarar kashe wani babban kwamandan kungiyar, Abu Hassan, tare da mayakansa 14.

Rahotanni sun ce sojojin da ke karkashin rundunar tsaro ta Operation Hadin Kai sun kashe Abu Hassan, wanda shi ne kwamandan Munzir.

Wani rahoton da aka tattaro na cewa an kashe ’yan ta’addan ne bayan wani soja daga cikin masu sintiri ya bude wuta a kan ’yan ta’addan.

A sakamakon hakan, sojojin sun yi amfani da bindigar kakkabo jirgi, wanda hakan ya yi sanadin halaka ’yan ta’adda 14 har lahira.

Zagazola Makama, kwararre a fannin yaki da tayar da kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro, ya rawaito cewa an kashe Abu Hassan, kwamandan da ya jagoranci tawagar mayakan kungiyar su 13.

“Daya daga cikin ’yan ta’addan da ke tattaunawa da wani Kwamandansu a sansanin Abu Iklima, an ji a asirce  yana cewa sojoji sun kashe mujahidanmu 13, ciki har da Abu Hassan.

“Wani ne ya harbe mu yayin da muke janyewa daga fagen daga a Ngowom, muna kan hanyarmu da gawarwakin, muna zuwa Gaizuwa.

“Abu Hassan ya kwanta dama, wasu daga cikin mayakanmu ma sun samu raunuka, muna iya neman taimakon gaggawa. Don Allah a kasance cikin shiri.”

Zagazola ya fahimci cewa har yanzu mayakan ba su isa Gaizuwa ba daga Bama har zuwa karfe 10:44 na ranar Talata, 15 ga Nuwamba.