✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojoji sun kashe mutum 70 a Binuwai

Wasu mutum 100 sun bace a samamen da sojojin suka kai bayan an kashe wasu dakaru

Sojoji sun hallaka kimanin mutum 70 a samamen da suka kai bisa zargin kashe mata dakaru 11 da aka yi a Jihar Binuwai.

Mazauna kauyen Mbator a yankin Shangev-Tiev na Karamar Hukumar ta Konshisha ne suka yi zargin a ranar Juma’a, da cewa wasu mutum 100 sun bace, baya ga mutum 70 da sojoji suka hallaka a samamen.

Aminiya ta ruwaito Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya na tabbatar da cewa wasu ’yan sa-kai a yankin sun kashe hafsanta daya da kananan sojoji 10 a lokacin da sojojin ke aikin wanzar da zaman lafiya.

Kauyukan Bonta da ke Mbatotar a Shangev-Tieve da kuma kauyen Okpute-Ainu a Karamar Hukumar Oju ta Jihar sun shekara fiye da 10 suna yakar juna a kan rikicin fili, wanda ke sanadiyyar girke sojoji domin kwantar da fitinar.

Rikicin ya sake tashi kwana biyar da suka gabata, wanda a sakamakonsa ne aka sake tura sojoji, amma wasu ’suka yi mutu kwanton bauna suka kashe 11 daga cikinsu, ciki har da hafson soji daya.

A dalilin haka ne sojoji suka kai samame a yankin, wanda mazauna ke zargin an da kashe wasu mutum 70, yayin da wasu 100 kuma ba a gan su ba.

Da take jawabi a garin Makurdi a ranar Juma’a, wata kungiyar mai suna Shangev-Tiev Assembly (STA) ta ce a kwana ukun da suka gabata, sojojin sun tarwatsa unguwanni 15 da ke makwabtaka da kauyen inda suka kai samame ta sama da kasa.

Ku dawo wa sojoji makamansu —Ortom ga sarakuna

Tuni Gwamnan Jihar Binuwai, Samuel Ortom ya umarci shugabannin al’aummar su tabbata sun shawo kan wadanda suka dauke makaman sojojin da aka kashe su dawo da su.

Sanarwar da ya fitar da kansa a ranar Juma’a ta kuma roki sojojin da mutanen yankin su kai zuciya nesa.

“A sakamakon rikici tsakanin al’ummomin Kananan Hukumomin Konshisha da Oju da ya sa aka a tura sojoji yankunan, ni da kai kaina, a madadin Gwamnatin Jihar Binuwai, ina rokon bangarorin biyu da kuma sojoji cewa su kai zuciya nesa.

“Na riga na umarci shugabannin al’ummomin cewa su tabbata an gaggauta dawo da makaman da aka dauke na sojojin da aka tura aikin samar da zaman lafiya a yankin.

“Ina kira ga mazauna yankunan da su fallasa wadanda suka kai wa sojojin hari haka kawai, saboda aikin ashha da suka yi, wanda ke neman gurgunta yunkurin samar da zaman lafiyaa a yankin.

“Sannan ina rokon sojoji da su guje wa taba fararen hula, su kare mutane masu bin doka a yayin da suke kokarin gano makaman nasu da aka dauke,” inji gwamnan.