✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kashe mayaƙan Boko Haram 10 a Borno

Bayan arangamar an samu makamai da yawa daga wurin, ciki har da bindigogin harbo jiragen sama.

Hedikwatar Tsaron Nijeriya (DHQ) ta ce dakarun tsaro na rundunar “Operation Hadin kai” sun kashe mayaƙan Boko Haram 10 yayin wata arangama a yankin Rann zuwa Gamboru Ngala da ke Jihar Borno.

Daraktan watsa labarai na hedikwatar tsaron, Manjo Janar Markus Kangye ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.

Manjo Janar Markus Kangye ya ce aikin kawar da ‘yan ta’addan da aka aiwatar ranar Litinin ya faru ne bayan rundunar ta lashi takobin kawar da sauran ‘yan Boko Haram/ISWAP da ke ɓuya a yankin Tafkin Chadi.

“Arangamar ta faru ne a lokacin wani aiki na haɗaka wanda aka shirya kuma aka aiwatar cikin dabara domin kawar da sauran ‘yan ta’addan Boko Haram/ISAWP da ke aika-aika a garuruwan da ke kan iyaka,” in ji Janar Kangye.

“Dakaraun da suka yi aiki bisa bayanan sirri sun danna cikin maɓuyar mayaƙan tsakanin Rann da Gamboru, inda suka yi ba-ta-kashi sannan suka kashe ‘yan ta’adda 10,” in ji sanarwar.

Ya ƙara da cewa bayan arangamar an samu makamai da yawa daga wurin, ciki har da bindigogin harbo jiragen sama.

Aikin wani ɓangare ne na dabarun karɓe iko da kudancin Tafkin Chadi da kuma hana zirga-zirgar ‘yan Boko Haram ta kan iyaka, a cewarsa.

“Ana nazari kan makaman da aka ƙwace yayin da ake ƙoƙarin gano waɗanda suka tsere da kuma sauran maɓoyar ’yan ta’adda a yankin,” in ji sanarwar.

Ya ƙara da cewa dakarun sojin Nijeriya, da haɗin gwiwar rundunar haɗin gwiwa ta MNJTF da kuma sauran jami’an tsaro sun zafafa ayyukansu a yankin Tafkin Chadi da sauran ɓangarori na arewacin Borno domin kakkaɓe sauran ‘yan Boko Haram a yankin