✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

Sojoji sun kashe mayakan ISWAP 8 a hanyar Maiduguri zuwa Damaturu 

Sojojin sun kuma kwato makamai da kayayyaki masu yawa daga hannunsu

Dakarun rundunar tsaro ta Operation Hadin Kai sun kashe wasu ’yan ta’addan ISWAP su takwas da suke kokarin kai hari a babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

Sojojin sun kuma samu nasarar kwato baburan hawa kimanin hudu da sauran kayayyaki  daga hannun maharan.

Wata majiya mai karfi ta tabbatar da cewa sojojin da ke sintiri na rundunar ta OPHK sun ci karo da ’yan ta’addan a wata mashiga ta garin Minok, wadanda suka yi yunkurin guduwa amma sojojin suka tare su cikin gaggawa tare da yi musu kofar rago suka kashe wasu daga cikinsu.

Kazalika, wata majiyar daga jami’an tsaro ta shaida wa Zagazola Makama, kwararre kan yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi, cewa sojojin sun halaka wasu ’yan ta’adda su takwas da ke kan babura hudu tare da kwato wasu kayayyaki masu tarin yawa daga hannunsu.

Majiyar ta ce, “Sauran kayayyakin da aka gano sun hada da magungunan karfin maza da na kashe kwari da kayan abinci da kuma makamai.

Kazalika, sojojijn sun kwace miyagun kwayoyi da sauran magungunan asibiti masu yawan gaske.

Majiyar ta ce ’yan ta’addan kan yi amfani da magungunan ne wajen jinyar mayakan da suka samu raunuka a wani kazamin fada tsakanin ISWAP da ’yan ta’addan Boko Haram a dajin Sambisa a cikin makon nan.