✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojoji sun kashe mayakan ISWAP 19 a Gamboru Ngala

Karo na biyu a kasa da kwana uku da sojoji suka yi raga-raga da ’yan ta'adda da suka kai musu harin kwanton bauna a yankin…

Sojojin Najeriya sun kashe mayakan ISWAP guda 19 bayan ’yan ta’addan sun yi musu kwanton bauna a garin Gamboru Ngala da ke kan iyakar Najeriya Jamhuriyar Kamar.

Ragargazar da sojojin tare da ’yan sa-kai Civilian JTF suka yi wa ’yan ta’addar a ranar Litinin a garin mai nisan kilomita 828 daga Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, ita ce ta biyu a cikin kasa da kwana uku.

Wata majiyar tsaro ta ce, da farko zugar mayakan dauke da muggan makamai sun bude wa sojojin wuta, “Amma dakarun suka fatatte su, suka kuma bi su suka kashe 19 daga cikinsu, amma ba su kashe soja ko daya ba, in banda wasu biyu da suka samu rauni.”

Majiyar ta ce bayan artabun na kusan minti 40, sojojin sun kwace bindigogi kirar AK 47 guda tara da  harsasai da mota a-kori-kura guda daya da babura guda tara wadanda ’yan ta’addar suka tsere suka bari.