Rundunar Tsaro ta Hadin Gwiwar Kasashe (MNJTF) da ke aiki a yankin Tabkin Chadi ta hallaka mayakan Boko Haram da na ISWAP 43 bayan wata musayar wuta a yankin Baroua da ke Diffa a Jamhuriyar Nijar a ranar Laraba.
Rundunar ta ce mutum bakwai daga cikin dakarunta sun kwanta dama sakamakon musayar wutar.
- Yadda Daruruwan Likitoci Ke Tururuwar Barin Najeriya
- Abubuwan da ya kamata ku sani a kan ranar Hausa
A cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na Rundunar da ke birnin Ndjamena a kasar Chadi, Kanar Muhammad Dole ya fitar, Rundunar ta ce dakarunta da ke garin Diffa na Jamhuriyar Nijar sun nuna jarumta lokacin da aka kai wa sansaninsu hari.
“Dakarunmu da aka girke a Baroua sun fuskanci wani hari daga wadanda muke kyautata zaton ’yan Boko Haram da ISWAP ne da safiyar ranar Laraba, 25 ga watan Agustan 2021.
“Sun samu galaba a kan ’yan ta’addan, sun kashe da dama daga cikinsu, yayin da wasu kuma suka tsere da raunukan harbi a jikkunansu.
“Sakamakon haka, an tsinci gawarwakin mutum 43 daga cikin wadanda muka hallaka a yankin.
“Kazalika, mun kama wani da muke zaton jagoransu ne da ransa da kuma tarin makamai da kuma wasu manyan bindigogi guda hudu.
“Sai dai muna bakin cikin sanar da cewa a sakamakon ba-ta-kashin, bakwai daga cikin hazikan dakarunmu sun ji munanan raunuka kuma suna samun kulawa a asibitin sojoji,” inji sanarwar.