Rundunar sojin sama ta Najeriya (NAF), ta samu nasarar kashe Ba’a Shuwa, wanda shi ne magajin tsohon shugaban kungiyar ta’adda ta Boko Haram, marigayi Abubakar Shekau.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, wannan nasara ta kashe magajin na Shekau na zuwa ne a sakamakon luguden wuta da sojojin ke yi babu kakkautawa kan ’yan ta’addan a Jihar Borno da sauran yankunan Arewa maso Gabashin Najeriya.
- ’Yan kwangila na buƙatar Naira tiriliyan 1.35 su kammala titin Kano zuwa Abuja
- Kotun Koli ta hana madugun adawar Senegal Ousmane Sonko tsayawa takara
Kafin rasuwarsa, Ba’a Shuwa shi ne shugaban Boko Haram a Najeriya da Tafkin Chadi da Kwalfarji da Timbuktu da kuma Sambisa hade da Kwamanda Mantika da ke da alaka da Ƙungiyar ta’adda ta ISWAP.
Wasu majiyoyin leken asiri sun shaida wa Zagazola Makama, wani kwararre a fannin yaki da tada kayar baya a yankin Tafkin Chadi cewa, munanan hare-haren da aka kai a ranar 2 ga watan Janairun 2024 a garin Kwatan Dilla da ke Karamar Hukumar Abadam ta Jihar Borno, ya kai ga kashe Ba’a Shuwa, tare da dimbin mayakansa.
An nada Shuwa ne a shekarar 2021 bayan mutuwar Abubakar Shekau wanda ya kashe kansa, inda ya kasance Kwamandan ‘yan ta’addan a garuruwan Chiralia, Markas Kauwa, Abirma, Buk, Abulam, Dusula, Abbagajiri, Gorgore da sauran sansanoni da dama a yankin Timbuktu da Alagarno a Kudancin Borno.
Wasu daga cikin manyan kwamandojin da harin ya rutsa da su sun hada da: Khaid Hanzala, Ba’a Idirisa, Rawana, Abou Ibrahim, Malam Abubakar, Abou Aisha da Abou Khalid wanda shi ne ke da alhakin harin da aka kai kan cibiyar wutar lantarki da ke kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.
Ba’a Shuwa na daga cikin ‘yan ta’addan da suka fi daukar alhakin kai hare-haren kwanton bauna da nakiyoyi a hanyoyin Damboa, Damaturu-Maiduguri, Askira, Buratai, Buni Yadi, Buni Gari, Geidam da sauran sassan jihohin Borno da Yobe.