Dakarun sojin Najeriya tare da mayakan sa-kai na Civilian JTF sun kashe kwamandojin kungiyar ISWAP guda biyu a yankin Yuwe na karamar hukumar Konduga ta Jihar Borno.
Kwamandojin da sojoji suka kashe a musayar wuta dai su ne Abu Huzaifa da wani Sarki da ya jagoranci kungiyar ISWAP a Dajin Sambisa kusan shekaru goma.
- An sako ragowar daliban FGC Birnin Yauri
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Kamata ’Yan Najeriya Su Koya Daga Rikicin Sudan
Wata kwakkwarar majiya ta bayyana cewa sojojin da ke aikin hadin gwiwa sun kuma “kashe ’yan ta’adda da dama yayin da wasu suka tsere raunukan harbin bindiga,” a artabun na ranar Asabar, 6 ga Mayu, 2023.
Ta ce, “Kwamanda ISWAP din da dakarun suka kashe, wato Sarki, ya jagorancin kai hare-hare da dama a Bita da Mubi da Adamawa da Madagali.
“Akwai karin wasu kamar su Abou Huzaifa, Abou Ubaida da Abba Tukur, wadanda su ma aka kashe.”
Majiyar ta kara da cewa, “Sojojin sun rasa daya daga cikin ’yan Civilian JTF, amma sun kwato alburusai da babura da kekuna takwas da kuma kayayyakin masarufi a wannan arangamar.”