✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojoji sun kashe kwamandan Boko Haram sun cafke 27

Sojoji sun kashe kashe Lawan Yashin sun kama Burama Modu dauke da katin zabe 67

Sojoji sun kashe shahararren dan ta’addan Boko Haram, Lawan Yashin, tare da cafke wani dauke katunan zabe 67  a sananin gudun hijira a Jihar Borno.

Hedikwatar Rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) da hadin gwiwar dakarun CJTF ta ce a ranar Alhamis ne suka kashe Lawan Yashin tare kuma da kama wani Burama Modu dauke da katin zabe 67 na dindindin a Maiduguri.

Daraktan yada labarai na tsaro, Manjo-Janar Danmadami Musa, ya ce an kashe Lawan Yashin ne a lokacin da yake kokarin tserewa bayan ya ga sojoji  tare da wasu 19 daga abokan ta’addancinsa a sansanin ’yan gudun hijira da ke Shuwari a Karamar Hukumar Maiduguri.

Manjo-Janar Danmadami Musa ya kara da cewa kana an kuma kama mutane 27 da ake zargin ’yan Boko Haram/ISWAP ne da kwato makamai da alburusai da daman gaske a hannunsu.

Ya bayyana cewa an kama wanda ake zargin da katunan zaben ne a sansanin ’yan gudun hijira da ke Shuwari kuma yana hannun sojoji domin amsa tambayoyi.

Ya yi wannan bayani ne a taron ’yan jarida kan sabbin ayyukan Rundunar Sojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro kan magance kalubalen tsaro tsakanin ranakun 20 ga Oktoba zuwa 3 ga watan Nuwamba, 2022.

A cewarsa, hare-haren da dakarun tsaron ke kaiwa sun yi nasarar kashe ’yan ta’adda da dama da kuma kwace manyan motoci masu dauke da bindigogi guda bakwai da sauran kayayyakin yaki mallakar’ yan ta’addar.

“Hakazalika, bisa sahihin bayanan sirri na ’yan ta’addan da ke yin sintiri a yankunan Abulum da Njibul da ke kusa da dajin Sambisa, rundunar ta kai farmaki a wuraren a lokaci guda tare da kashe ’yan ta’adda da dama, yayin da aka ga wadanda suka ji rauni sun ranta a na kare,” in ji shi.

Janar Danmadami ya kuma bayyana cewa, a tsawon lokacin ’yan ta’addan Boko Haram 145 da iyalansu, maza 30, mata 33 da kananan yara 82 ne suka mika wuya ga sojoji a wurare daban-daban a Arewa maso Gabas.”

Babban kwamandan sojojin ya yaba wa kokarin da sojojin ke yi a bangarori daban-daban a fadin Najeriya .

%d bloggers like this: