✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojoji sun kashe jagororin IPOB 13

Sojoji sun kwato akwatin zabe da na'urar rajistar masu zabe da sauran abubuwa a hannun miyagun da suka addabi yankin Kudu maso Gabas

Sojojin Najeriya sun kashe wasu kwamandoji 13 na kungiyar ta’addanci ta IPOB a yankin Kudu maso Gabas.

Dakarun sun kuma cafke bokan IPOB tare da wasu ’yan kungiyar su biyar, inda suka kwato na’urar rajistar masu zabe a yayin zagargazar da suke ci gaba da yi wa ’yan ta’addan a yankin.

Daraktan Yada Labarai na Rundunar Tsaro ta Najeriya, Birgediya-Janar Musa Danmadami, ya ce, “A mako guda mun kashe jagororin IPOB 13, muka cafke wasu shida, ciki har da bokan kungiyar.

“Mun kwato bindigogi 15 da albarusai iri-iri da kuma kaki da sauran kayayyakin soji a hannunsu.

“Sauran sun hada da akwatin zabe da na’urar rajistar masu zabe na Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da na’urorin sadarwa da motoci da sauransu.”

Birgediya-Janar Musa Danmadami ya ce tuni sojojin suka mika ’yan ta’addan na IPOB da kayayyakin da aka kwace a hannunsu ga hukumomin da suka dace domin gurfanar da su a kotu, saboda su girbi abin da suka shuka.