✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kashe jagoran ’yan bindigar Kaduna Danwasa

El-Rufai ya yaba wa kwazon sojojin na ci gaba da tabbatar da tsaro a fadin Jihar.

Dakarun Sojin Operation Forest Sanity (OPFS) sun kashe wani kasurgumin jagoran ’yan bindigan Jihar Kaduna, Isiya Danwasa da abokinsa.

A cewar Kwan Tsaro da Harkokin Cikin cikin gida, Samuel Aruwan, Danwasa ne yake jagorantar kashe-kashe da garkuwa da mutane da kuma satar shanu a fadin jihar.

Aruwan, ya ce Danwasa ya gamu da ajalinsa ne a wani harin kwanton-bauna da suka kai a yankin Sabon Birni a Karamar Hukumar Igabi.

“Gwamna El-Rufai ya yaba wa sojojin bisa kwazon da suka yi wanda ya kai ga nasarar kashe Danwasa da abokinsa,” in ji shi.

Ya kara da cewa gwamnan ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da bayanan da za su taimaka wajen ci gaba da samun nasarar yaki da ta’addanci a jihar.