✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kashe gomman ’yan ta’adda a Zamfara

Sojoji sun shafe yini biyu suna artabu da ’yan bindigar a yankin.

Sojojin rundunar Operation Hadarin Daji sun samu nasarar kashe ’yan bindiga da dama a dajin Gadar Zaima da ke Karamar Hukumar Bukkuyum ta Jihar Zamfara.

Majiyarmu ta ce, sojojin sun shafe yini biyu suna artabu da ’yan bindigar a yankin.

Bayanai sun nuna yayin samamen, sojojin sun samu nasarar kwace babura sama da 100 da shanu kimanin 600 daga wajen ’yan fashin dajin.

Wannan na zuwa ne, bayan kai hare-hare ba kakkautawa da ’yan bindigar karkashin jagorancin shugabansu Buzu suka rika kai wa kauyuka da ke kananan hukumomin, inda sun hallaka gommai kuma da dama sun jikkata.

Gagarumar nasarar da sojojin suka samu ta yi matukar faranta wa mazauna yankunan kananan hukumomin Bukkuyum da Gummi.

Aminiya ta gano cewa, sojojin sun tare ’yan bindigar ne a mayan motoci makare da shanu, a kauyen Zugun Kebbe da ke kusa da iyakar Jihar Sakkwato, daura da dajin Dan Marke.

Rahotanni sun ce a baya-bayan nan, ’yan bindigar sun addabi yankunan da lamarin ya shafa wanda ya kai ga ba sa iya barci idanunsu rufe.

An kashe mutane da dama, da yawa sun tsere neman mafaka a wasu kauyaka sakamakon hare-haren kasurgumin dan ta’adda Buzu da mabiyansa.

Wani mazaunin kauyen da lamarin ya faru mai suna Usman, ya bayyana mana cewa an samu musayar wuta tsakaninsu, har sojojin suka harbe da dama daga ’yan bindigar.

“Akwai gawarwaki da muka gani a baje a inda aka yi musayar wutar.

“Sannan akwai wasu ’yan bindigar ma da suka dawo kwashe gawarwakin ’yan uwansu da su ma sojin suka harbe su.

Aminiya ta yi yunkurin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ‘Operation Hadarin Daji’, Kyaftin Ibrahim Yahaya, sai dai hakan ya ci tura, saboda gaza samunsa a waya.