Rahotanni sun ce sojoji sun kashe ’yan bindiga da dama yayin wani artabu a ƙauyen Gudiri da ke gundumar Bashar a Ƙaramar Hukumar Wase ta Jihar Filato.
Lamarin ya faru ne kwanaki biyu bayan da sojoji suka tsinci gawar ɗan sandan da aka yi garkuwa da shi a ranar Larabar makon jiya a kewayen ƙauyen Kampani da ke gundumar a wani daji.
Mazauna unguwar sun shaida wa Aminiya cewa, arangamar baya-bayan nan ta faru ne da yammacin ranar Litinin, inda sojoji da ’yan banga suka kai wa shugaban ’yan fashin farmaki bayan da aka samu rahoton hare-haren ’yan bindiga a yankin.
Sun ƙara da cewa jami’an tsaro sun yi nasarar fatattakar ’yan bindigar daga maɓoyarsu.
Mazauna yankin sun ce an ƙwato shanu sama da 100 da ake zargin na sata ne daga hannun ’yan bindigar bayan samamen.
Kakakin Rundunar Operation Safe Haven sa ke aikin wanzar da zaman lafiya a jihar, Manjo Samson Zhakom, bai amsa kiran waya ko amsa saƙon da wakilinmu ya aika masa ba.
Shapi’i Sambo, shugaban matasa a Wase, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce kodayake bai iya tantance adadin waɗanda suka mutu a lamarin ba, amma dai an kashe ’yan bindiga da dama a lokacin da sojoji suka kai farmaki a sansaninsu.
Da yake bayyana yadda lamarin ya faru, shugaban matasan ya ce, “Bayan sun samu rahotannin hare-haren ta’addanci da ’yan bindigar ke aikatawa a kullum, sai jami’an tsaro suka shiga yankin don kawar da su.
“An kashe da yawa daga cikin ’yan bindigar yayin da wasu suka tsere.”