Wasu hare-hare da jiragen yakin sojojin saman Najeriya suka kai sun kashe mayakan ISWAP da ba a tantance adadinsu ba a yankunan Turo da Ambia na Karamar Hukumar Gujba da ke Jihar Yobe.
Majiyar tsaron ta bayyana cewar, sojojin saman da ke sintirin leken asiri sun samu nasarar kashe ’yan ta’addar ne da yammacin ranar Litinin bayan da jirgin saman yakin ya kai hari a matsugunnin mayakan.
- Fara fiffiken tururuwa: Fadar tsohon Sarki Sunusi a Kaduna
- Kwana 6 kafin saukar Buhari NNPC ya ci gaba da hako mai a Borno
Majiyar ta shaida wa Zagazola Makama, kwararren mai sharhi kan yaki da tada kayar baya da harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi cewa an kai harin ne ta sama biyo bayan binciken da sojojin suka gudanar.
A cewar Makama, binciken ya nuna wasu manyan motocin masu dauke da bindigogi guda takwas na jigilar mayakan zuwa wani wuri da ake kyautata zaton hari suke da kudirin kaiwa.
Bayanai sun ce da yawa daga cikin mayakan sun hallaka sakamakon wannan hari ta sama da dakarun sojin suka kai musu da sabbin jiragen yaki na Tucano.