✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Fara fiffiken tururuwa: Fadar tsohon Sarki Sunusi a Kaduna

Gwamnatin Kano ta tsige Sanusi ta kuma tura shi gudun hijira wani kauye a Jihar Nasarawa.

Turawan Mulkin Mallaka sun tumbuke sarakuna da dama a farkon zuwansu, suka kuma kai su Lakwaja gudun hijira.

Bayan samun ’yancin kai a 1960, Gwamnatin Arewa ta warware rawanin Sarkin Kano Sanusi na I, ta kuma tura shi gudun hijira Azare.

Daga baya Gwamnatin Kano ta dawo da shi garin Wudil.

Da wayonmu, mun ga an sauke Sarkin Muri ga Sarkin Musulmi Ibrahim Dasuƙi da kuma Sarkin Gwandu Jokolo.

Duk cikin sarakunan da aka sauke daga gadon sarauta tun farkon zuwan Turawa ba mu taba gani ko jin abubuwan da muke gani da jin labari a yau ba na tawaye da sunan wayewa wadda samun wuri ya haifar.

Gwamnatin Kano ta tsige Sanusi ta kuma tura shi gudun hijira wani kauye a Jihar Nasarawa.

Abokinsa Gwamnan Jihar Kaduna ya tashi takanas ta Kano, ya je har kauyen ya dauko shi. Sanusi ya koma Legas da zama.

Masoya da magoya baya suna ganin hakan ya yi daidai.

Da sannu-sannu Sarkin Kano na 14 ya mayar da Kaduna, inda abokinsa ke Gwamna, sabuwar masarautarsa.

Yana shigar alfarma irin ta sarakuna masu ci, kuma yana tafiya da fadawa, dogarai da kuma zagage.

Wadannan abubuwan da yake yi, babu wani Sarki da aka tube a tarihin kasar nan tun zamanin Turawa zuwa yau da ya taba yi.

Masoya da masu goyon baya ba sa ganin matsala da wannan sabuwar bidi’ar da Muhammdu Sunusi ke kokarin sunnantawa.

Yanzu wannan ya fara zama irin na fada a Kaduna ta kasar Zazzau inda abokinsa ke Gwamna.

Ba zaman fadar a Kaduna ta kasar Zazzau ba ce abar damuwar mai rubutu, halartar Sarkin Zazzau mai ci da fadawansa fadar ce abar damuwar.

Da takaici Sarkin Zazzau, Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kaduna, ya ziyarci fadar tsohon Sarkin Kano a Kaduna, ya kuma zauna bisa kujerar baki dogaransa na zube a kasa, shi kuma Sunusi na bisa karaga yana sarautar hotiho a cikin kasar Zazzau!

Ko ba komai wane irin sako Masarautar Zazzau ke kokarin aika wa Sarkin Kano mai ci a yau?

Ba laifi ba ne Ambasada Ahmad Bamalli ya ziyarci Sanusi a matsayin abokinsa ko ubangidansa ko abokin ubangidansa Gwamna a matsayinsa na Ahmad Bamalli.

Amma Sarkin Zazzau mai ci a fadar tsohon Sarki, bisa kujerar manyan baki a kasar Zazzau abin dubawa ne!

Masarautar Zazzau, kamar kowace masaurata a Arewa, da ma duniya, na da martaba da kuma tsarin sarauta wanda ake kiyayewa, kuma duk dan Sarkin da ya san sarauta, ya san su kuma yana girmama su, ba zai taba yi masu karantsaye ba.

Ina ganin ya kamata dattawan Masarautar Zazzau su zauna da Sarkin Zazzau su ankarar da shi cewa Sarautar Zazzau kafaffiyar masarauta ce ba je-ka-na-yi-ka ba, duk da mutane da dama na ganin nadinsa a hakan.

Saboda haka kada neman yardar wani ko neman dadada wa wani ko son burge wani su sa ya ja girma da daraja da kimar masarautar Zazzau cikin juji.

Allah ke ba da mulki Ya ba shi, kada ya dauka zama dan barandar wani ne zai dawwamar da shi a bisa gadon sarautar.

Haka ya zama wajibi ga dattawan Arewa, musamman masu goyon bayan ci gaban tsarin sarautun gargajiya, su cire tsoro ko kwadayi ko neman yarda, su taka wa Sanusi na II birki.

Su ankarar da shi cewa duk yadda kake maita da kulafucin son abu, in ya fita hannunka ya koma ga waninka, dole ka kaurace wa yin duk wani abu da zai zubar ko rage girma da kimar wannan abin da ka rasa kuma kake masifar so.

Masoyan Sanusi na yi masa fata ya zama dambu mai hawa biyu.

Yaya zai ji idan ya koma sarautar Kano a gobe, sannan wanda aka cire shi ma ya rika yin irin abubuwan da yake yi a yanzu?

Muddin ba a yi wa wannan tufkar hanci ba, to akwai yiwuwar wata rana a tsige wani daga sarauta, in yana da kudi da karfin fada-a-ji da kuma abokai gwamnoni, ya zo cikin garin da aka cire shi sarautar, ya gina kasaitacciyar fadar alfarma, ya fid da kudi shi ma ya dauki dogarai da zagage da ’yan barda ya kuma rika gayyato abokansa sarakuna daga wasu masarautu su rika kawo masa ziyarar girmamawa!

Aliyu Ammani, U/Shanu Kaduna. [email protected].