✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kashe ɗan ta’adda da aka sa ladar N100m a kansa a Borno

Sojoji sun kama Abu Fatima wanda aka sanya ladar Naira miliyan 100 ga duk wanda ya kamo shi, da ransa a wani a yankin Arewacin…

Sojojin Najeriya sun kashe wani ƙasurgumin kwamandan ’yan ta’adda mai Amir Abu Fatima da aka sanya ladar Naira miliyan 100 ga duk wanda ya kama shi ko ya tona asirin inda yake, aka kama shi.

Sojoji sun kama Abu Fatima ne da ransa bayan musayar wuta a wani samame na musamman a safiyar Juma’a a yankin Kukawa da ke yankin Tafkin Chadi a Arewacin Jihar Borno.

Daga bisani ya mutu a hannun sojoji a sakamakon zubar da jini fiye da ƙima daga raunukan harbi da ya samu a yayin musayar wuta.

Majiyar leken asiri tabbatar da cewa, a yayin samamen, sojoji sun mataimakin Abu Fatima da masu haɗa ababen fashewa da mayaƙa da dama a maɓoyar tasu.

Dakaru na musamman sun kutsa cikin yankin da ’yan ta’addan suke  inda suka yi artabu da su a wani kazamin musayar wuta.

Kayayyakin da sojojin suka ƙwato sun hada da bindigogi kirar AK-47 da dama, da akwatunan harsasai  masu yawa, da kayan ƙera bama-bamai, da sauran kayan yaƙi.

Abu Fatima yana daga cikin jerin ’yan ta’addan da jami’an tsaro ke nema ruwa a jallo saboda hannu a hare-haren ta’addanci a yankin Tafkin Chadi.

Ana kallon mutuwarsa a matsayin wani babban koma baya ga ayyukan ’yan ta’adda da suka hana al’ummomin yankin sakat.