✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojoji sun kama ‘yan kungiyar asiri 61 a Kuros Riba

Dubun wasu ‘yan kungiyar asiri ya cika bayan sojoji sun yi musu dirar mikiya a yayin da suke taro a maboyarsu a jihar Kuros Riba.…

Dubun wasu ‘yan kungiyar asiri ya cika bayan sojoji sun yi musu dirar mikiya a yayin da suke taro a maboyarsu a jihar Kuros Riba.

Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya shiyyar, Kudu maso gabas da ke Kalaba ce ta yi nasarar kama matasan su 61.

Ana zargin su da ayyukan kungiyar asiri a sassan jihar ta Kuros Riba.

An kama su ne a maboyarsu yayin rantsar da sabbin shiga kungiyar a kungurmin dajin Akpabuyo da ke karamar hukumar Akpabuyo.

A makon da ya gabata gwamnatin jahar ta fitar da sunayen wasu mutum 35 da take zargi da addabar mazauna jihar da yawan fadace-fadace a garin Kalaba.

Lamarin ya fara ne da matsalar garkuwa da mutane domin kudin fansa da kuma fadace-fadacen kungiyoyin asiri.

Da yake mika wa hukumar ‘yan sanda wadanda ake zargin, kwamandan sojan ruwa Rear Admiral Vincent Okeke da Kyaftin Ibrahim Gwaska ya wakilta, ya ce wasu mutanen kirki ne suka kyankyasa musu, sannan suka kai samamen da ya kai ga cafke mutum 61.

Ya kara da 42 daga cikin matasan sun yi ikirarin su ‘yan kungiyar asiri ta ‘Klans’ da ‘Black Axe’ da ke halartar rantsar da sabbin shiga kungiyar.

Da yake karbar su Mataimaki na Musamman kan Harkokin Tsaro Shiyyar Kudancin jihar Kuros Riba,  Ani Esin ya yaba wa hukumar sojin ruwan tare da alkawarin gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.