✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kama mai tattara wa Boko Haram bayanai a tsakiyar Abuja

Ana zarginsa da zama yaron wani kwamandan Boko Haram a Kaduna

Dakarun sojojin Najeriya sun cafke wani mai samar wa ’yan ta’addan Boko Haram bayanai a unguwar Asokoro da ke tsakiyar Babban Birnin Tarayya Abuja, mai suna Mamuda Usman, wanda aka fi sani da Bado.

A cewar sojojin, ana zargin bado ne da kasancewa dan aike ga wani babban kwamandan ’yan ta’addan da ke Kaduna, wanda kuma yake cikin jerin mutanen da jami’an tsaro ke nema rauwa a jallo.

Daraktan Yada Labarai na Hedkwatar Tsaro ta Kasa, Manjo Janar Musa Danmadami, ne ya bayyana hakan a Abuja, lokacin da yake jawabi ga manema labarai a ranar Alhamis.

Bayanin na zuwa ne kasa da sa’o’i 48 bayan Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS ta cafke fitaccen dan jaridar nan na Kaduna, kuma mawallafin jaridar Desert Herald, Tukur Mamu, saboda zarginsa da hannu a badakalar kudaden fansa da suka kai Naira biliyan biyu.

A cewar Manjo Janar Danmadami, “Dakarunmu na musamman sun kama mai samar wa Boko Haram da bayanai mai suna Mamuda Usman (wanda aka fi sani da Bado) a unguwar Asokoro da ke Abuja.”

Ya kuma ce yanzu haka Badon yana hannunsu inda ake ci gaba da bincikensa.

Har ila yau, ya ce a dai ranar da aka kama shi, dakarunsu sun kuma sami rahoton wani satar mutane a kauyen Changal da ke karamar hukumar Mangu da kauyen Pinau da ke karamar hukumar WasE a jihar Filato.

Ya ce cikin gaggawa dakarun nasu suka sami nasarar kubutar da mutanen tare kuma da ceto su, yayin da su kuma ’yan ta’addan suka ranta a na kare.