✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kama jirgin ruwa makare da lita 350,000 na man dizel din sata

Sojojin sun ce suna zargin man da aka samu na sata ne.

Rundunar Sojojin Ruwan Najeriya a Fatakwal, Jihar Ribas sun kama wani jirgin ruwa mai suna MV Cecilia dauke da kusan lita 350,000 na dizel da ake zargin na sata ne.

Kwamandan rundunar tsaro ta Operation Delta Safe (OPDS), Real Admiral Olusegun Ferrera, ne ya sanar da hakan a ranar Laraba.

Ferrera, wanda ya samu wakilcin Kwamandan bangaren ruwa na rundunar hadin gwiwa ta Kudu Maso Kudu, Commodore Adedokun Siyanbade, ya bayyana hakan ga manema labarai.

Ya ce jirgin da ba a yi amfani da shi ba tsawon ba shekaru biyu, an kai shi wani wajen ajiyar kayayyaki ba bisa ka’ida ba.

A cewar kwamandan, a wani bangare na kokarin inganta da tabbatar da tsarin aiki, kwamandan rundunar hadin gwiwar, ya umarci rundunar da ta gudanar da bincike a yankin.

Ya ce sun samu bayanan sirri cewa ana tafka ta’asa a yankin, inda ya kara da cewa farmakin da aka gudanar a ranar 15 ga watan Agusta, 2023, ya kai ga kama jirgin na MV Cecilia.

Ya ce, “Na zo nan ne a madadin kwamandan rundunar hadin gwiwa ta Operation Delta Safe, Real Admiral Olusegun Ferrera. Mun zo da safiyar yau ne don nuna muku yadda aka kama wani jirgin ruwa da ke yin aiki ta haramtacciyar hanya a wannan yanki.

“An gudanar da aikin ne a jiya, 15 ga watan Agusta, 2023 kuma an kai ga kama MV Cecilia tare da wani jirgin ruwa wanda ya kamata ace yana aiki amma an mayar da shi tankin ajiyar haramtattun kayayyaki. Mun samu litar dizal kusan 350,000 a ciki.

“An kama su ne suna dibar danyen mai daga wani rami da aka tona a yankin Obio general na jihar Ribas.

“Don haka, wannan jirgin ruwa da wadancan tankunan za a gudanar da bincike a kansu.”

Ya ce wadanda ake zargin da kuma jirgin ruwa da kayayyakin za a mika su ga hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) don fadada bincike.